Majalisar dattawa ta amince da cin bashin dala biliyan 5.5 da shugaban kasa Muhamadu Buhari ya nemi su bada izinin ciyowa ranar talata 14 ga watan nuwamba yayin da suke zaman majalisa.
A zaman su ranar talata, shugaban kwamitin bashin cikin gida da na kasashen waje sanata Shehu Sani ya kaddamar da rahoton kwamiti dinsa ga sauran yan majalisa.
A rahoton sa, Shehu Sani yace bayan ganawar shi da ministan sufuri Rotimi Ameachi da wasu yan majalisar zartarwa na shugaban kasa kan amfanin bashin da za'a ciyo, kwamiti dinshi nada tabbaci cewa ayyukan da za'a gabatar da bashin zai taimaka wajen bunkasa cigaban kasuwanci tare da samad da aiki ga dinbim yan kasar.
A ranar talatan ne shugaban majalisar dattawan ya karanta wasikar neman izini kan cin bashin $5.5B da shugaban kasa ya tura wanda dashi za'a gabatar da wasu ayyuka na daga cikin kasafin kudin bana.
A bisa kididdigi da hukumar dake kula da basusuka ta walafa cikin watan satumba, adadin bashin da kasar Nijeriya ta ciyo ta tashi zuwa 61.96% tunda shugaba Muhammadu Buhari ya hau kujerar mulki.
Yan majalisar dattawa sun amince da bashin $5.5B da shugaba Buhari ke neman izinin samowa
Reviewed by Martbiz.blospot.com
on
November 14, 2017
Rating:
No comments: